1 Peter 2

1Saboda haka, ku rabu da kowace ƙeta da dukan ruɗu, munafunci, kishi, da kuma kowace irin ɓata suna. 2Kamar sababbin jarirai, ku yi marmarin madara tsantsa ta ruhaniya, domin ta wurinta za ku yi girma cikin cetonku, 3yanzu da kuka ɗanɗana alherin Ubangiji.

Dutse Mai Rai da kuma Zaɓaɓɓun Mutane

4Da kuka zo gare shi, rayayyen Dutse-da mutane suka ƙi amma Allah ya zaɓa, kuma mai daraja a gare shi—  5ku ma, a matsayinku na duwatsu masu rai, ana gina ku ga zama gidan ruhaniya don ku zama tsattsarkar ƙungiyar firistoci, kuna miƙa hadayun ruhaniya, abin karɓa ga Allah ta wurin Yesu Kiristi. 6Gama a cikin Nassi an ce,

“Ga shi, na kafa dutse a Sihiyona,
zaɓaɓɓen dutse na kusurwar gini mai daraja,
wanda kuma ya dogara gare shi
ba zai taɓa kunyata ba.”
Ish 28.16

7A gare ku da kuka gaskata, wannan dutse mai daraja ne. Amma ga waɗanda ba su gaskata ba,

“Dutsen da magina suka ƙi
ya zama dutsen kusurwar gini,
Zab 118.22

8kuma,

“Dutse ne da yake sa mutane tuntuɓe
kuma fā ne da yake sa su fāɗi.”
Ish 8.14

Sun yi tuntuɓe domin sun ƙi su yi biyayya da saƙon-wanda kuma yake abin da aka ƙaddara musu.

9Amma ku zaɓaɓɓu ne, ƙungiyar firistocin babban Sarki, alʼumma mai tsarki, jamaʼa mallakar Allah, domin ku shaida yabon shi wanda ya kira ku daga cikin duhu zuwa haskensa mai banmamaki. 10Dā ku ba mutane ba ne, amma yanzu ku mutanen Allah ne; Dā ba ku karɓi jinƙai ba, amma yanzu kun karɓi jinƙai.

11Abokaina ƙaunatattu, ina roƙonku, a matsayin bare da kuma baƙi a duniya, ku rabu da shaʼawace-shaʼawacen zunubin da suke yaƙi da ranku. 12Ku yi irin rayuwa mai kyau a cikin masu bautar gumaka, yadda ko da sun zarge ku da yin laifi, za su iya ganin ayyukanku nagari, su ɗaukaka Allah a ranar da zai ziyarce mu.

Biyayya ga Masu Mulki da Iyayengiji

13Saboda Ubangiji, ku yi biyayya ga kowace hukumar da aka kafa cikin mutane: ko ga sarki, a matsayi wanda ya fi iko, 14ko ga gwamnoni, waɗanda ya aika domin su hukunta masu laifi su kuma yabi masu aikata abin da yake daidai. 15Gama nufin Allah ne cewa ta wurin yin nagarta za ku toshe jahilcin marasa azanci. 16Ku yi rayuwa kamar mutanen da aka ʼyantar, sai dai kada ku yi amfani da ʼyancinku a matsayin hujjar aikata mugunta; ku yi rayuwa kamar bayin Allah. 17Ku nuna ladabin da ya dace ga kowa: Ku ƙaunaci ʼyanʼuwantakar masu bi, ku ji tsoron Allah, ku girmama sarki.

18Bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku da matuƙar ladabi, ba kawai ga waɗanda suke da kirki da masu sauƙinkai ba, amma har ga masu zafin rai ma. 19Gama abin yabo ne in mutum ya yi haƙuri cikin zafin wahalar rashin adalci saboda yana sane da Allah. 20Amma ina abin taƙama in kuka sha duka saboda kun yi laifi kuka kuma jimre? Sai dai in kuka sha wahala saboda yin nagari kuka kuma jimre, abin yabo ne a gaban Allah. 21Ga wannan ne aka kira ku, domin Kiristi ya sha wahala dominku, ya bar muku gurbin da ya kamata ku bi.

22“Bai taɓa yin laifi ba sam,
ba a kuma sami ƙarya a bakinsa ba.”
Ish 53.9

23Saʼad da suka zazzage shi, bai rama ba; saʼad da ya sha wahala, bai yi barazana ba. A maimakon haka, ya miƙa kansa ga wanda yake shariʼar adalci. 24Shi kansa ya ɗauki zunubanmu a jikinsa a kan itace, domin mu mutu ga zunubai mu kuma rayu ga adalci; ta wurin raunukansa ne kuka sami warkarwa. 25Gama dā kuna kama da tumakin da suka ɓace, amma yanzu kun dawo ga Makiyayi da kuma Mai lura da rayukanku.

Copyright information for HauSRK